Ma’aikatanmu
Babban Edita/Shugaba

Bashir Sa’ad Abdullahi, tsohon Edita ne na ofishin tashar BBC World Service a Abuja, babban birnin Najeriya. Yana da kwarewa ta fiye da shekara 15 a fanni daban-daban na aikin jarida, musamman hanyoyin zamani na aikin da shafukan intanet da na sada zumunta da kuma jagorancin kafofin sadarwa da na yada labarai. Bashir a halin yanzu yana gudanar da aikin binciken digiri na uku ko digirin digirgir (PhD) a jami’ar Westminster da ke Landan, a Burtaniya. Binciken nasa ya ta’allaka ne a fannin yadda ake yada labaran karya da kuma hanyoyin dakile su a nahiyar Afirka. Kafin nan, Bashir ya samu digirinsa na biyu a fannin gudanar da kamfanoni (MBA) a kasar Saudiyya da kuma wani digirin na biyu a fannin aikin jarida daga Jami’ar Westminster a Burtaniya. Ya kuma yi digirinsa na farko ne a tsangayar koyar da aikin jarida da ke Jami’ar Bayero, a Kano, Najeriya. Za a iya tuntubarsa a adireshinsa na email: elbashirkano@gmail.com
Edita/Babban Darakta

Ibrahim Shehu Adamu kwararren dan jarida ne da ya yi kusan shekara 20 yana aikin a fannoni daban-daban. Edita ne na hada shirin labarai kai tsaye a gidan talbijin na Turkiyya da ke watsa shirye-shirye a harshen Turanci wato TRT World. Kafin nan kuma ya yi aiki a bangaren talbijin na BBC World a matsayin babban mai hada shirin BBC Focus on Africa. Har ila yau ya yi aiki a bangaren radiyo na BBC Focus on Africa da Newsday - duka a London. A lokacin da yake Najeriya, ya yi aiki da sashen Hausa na BBC a bangaren rediyo da kuma kafafen sadarwa na zamani. Ibrahim Shehu Adamu ya yi aiki a gidan rediyon Nagarta da babban gidan talbijin na Najeriya NTA, duka a Kaduna a matsayin mai aiko da rahotanni. Yana da shaidar karatu ta HND a Mass Communication daga Kwalegin Kimiyya da Fasaha ta Kaduna. Kuma yana da shaidar kwarewa a fannin shugabanci daga Cibiyar IBMI da ke Berlin, Jamus. Za ku iya tuntubarsa a adreshin email a: Ibrahim4shehu@gmail.com
Mai Kula da Harkokin Gudanarwa

Shehu Sani Shehu ya sami kwarewa da gogewa akan harkar shugabanci da gudanarwa cikin sama da shekaru 12 da ya shafe yana aikin gudanar da mulki har ya kai mataimakin Darakta a karkashin gwamnatin jihar Kano, Najeriya. Ya yi aiki a ma’aikatu daban-daban wadanda ke gudanar da ayyuka mabambanta kuma hakan ya bashi damar samun kwarewa akan tafiyar da ma’aikatu da gudanar da mulki da tsare-tsare. Shehu dan jarida ne mai zaman kansa wanda ya yi aiki da kafar yada labarai ta BBC Monitoring (wadda ke bibiya da gabatar da rahoto akan kafafen yada labarai da ke sassan duniya), hakan ya bashi damar samun kwarewa akan aikin fassarar labarai da rahotannin kafafen yada labarai na gargajiya da na zamani. Yana da shaidar karatu ta digiri na biyu da na farko akan ilimin aikin jarida da tsare-tsare daga jami’ar Bayero a jihar Kanon Najeriya. Yana da ra’ayin bincike akan aikin sadarwa da irin yadda shugabanni ko masu fada aji ke amfani da kafafen yada labarai wajen yin sharhi akan rahotannin da ake yadawa domin cimma muradunsu. Shehu mamba ne a hukumar kwararru ta masana harkokin tallace-tallace ta Najeriya (Advertizing Practitioners Council of Nigeria - APCON). Za iya samunsa kai tsaye a: shehusshehu79@gmail.com
Marubuci
Umar Mikail Abubakar matashin dan jarida ne da ke da kwarewa a kan kafofin sada zumunta da kuma intanet baki daya. Ya kuma kware sosai wajen tantance labaran boge da kuma yin binciken kwakwaf. Bayan kammala digiransa a jami'ar Maitama Sule da ke Kano, inda ya karanci harshen Ingilishi, Umar ya shafe watanni yana koyon aiki a jaridar Daily Trust da kuma Aminiya a Abuja, Najeriya. Kafin daga bisani ya koma kafar yada labarai ta BBC, inda ya kasance cikin jerin wadanda suka bayar da rahotanni masu kayatarwa a kan zabukan Najeriya na 2019 da kuma gasar cin kofin kasashen Afirka. Hakan ne ya sa aka bashi damar ci gaba da yin aiki na wucin-gadi a ofishin BBC da ke Abuja, inda yake cikin masu kula da shafukan intanet na BBC Hausa. Ya dade yana yin rubutu ga shafin Bindiddigi. Za a iya tuntubarsa a umarmikail1@gmail.com